Nana Akufo-Addo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Nana Addo Dankwa Akufo-Addo



Nana Addo Dankwa Akufo-Addo
Hoto: The Presidecny, Ghana

Gabatarwa

Mai Girma Shugaban Ƙasar Ghana, Nana Akufo-Addo. Shugaba, Basarake, Fitaccen Lauya, Gogaggen Ɗansiyasa, kuma Jajirtaccen Ɗan Rajin Ƙwatar ‘Yanci.

Ya yi karatu tun daga matakin farko har zuwa matakin digiri a gida Ghana da kuma Ingila. Ya bayar da gagarumar gudunmawa tare kuma da cigaba da bayar da wannan gudunmawa bakin rai bakin fama wajen ganin Ghana da al’ummarta sun cigaba da nufin ɗorawa daga gurin da mahaifinsa ya tsaya, wanda yake ɗaya ne daga cikin Turaku-Shida (The Big-Six) da suka assasa fafutikar ƙwatar ‘yancin kai a Ghana da ma faɗin Afirka baki ɗaya, wato Marigayi Tsohon Shugaban Ƙasar Ghana Maras Cikakken Iko, Edward Akufo-Addo. Madalla da wannan ɗan kishin ƙasa Nana Akufo-Addo wanda wannan rubutu yake son baka labarinsa. A sha karatu lafiya.

Haihuwa

An haifi Nana Akufo-Addo a unguwar Swalaba da ke Birnin Accra wanda kuma nan ne babban birnin Ƙasar Ghana, a ranar 29 ga watan Maris na shekarar 1944. Cikakken sunansa shi ne Nana Addo Dankwa Akufo-Addo.

Ya gaji siyasa zamowarsa ɗa ga Edward Akufo-Addo; tsohon Babban Jojin Ƙasar Ghana na uku a tarihi; Tsohon Shugaban Ƙasar Ghana Maras Cikakken Iko (1970 – 1972); kuma ɗaya daga cikin Turaku-Shida (The Big-Six) da suka jagoranci fafutikar samun ‘yancin kan Ghana a matakin farko, daga baya kuma Afirka baki ɗaya, sannan kuma waɗanda ake maƙala hotunansu a jikin kuɗaɗen Ƙasar Ghana


Fuskokin Turaku Shidan Ghana a Jikin Kuɗin Ghana
Hoto:Babban Bankin Ghana

Basarake ne shi bisa gado kasantuwarsa ɗa ga Adeline Akufo-Addo wadda ita kuma take ‘ya ga sarkin Asante Acim Abakwa (Akyem Abuakwa), Nana Sir Ofori Atta. Dalilin da ya saka ake yi masa laƙabi da Nana.

Karatu

  • 1957: Accra Government Boys School da Rowe Road School duk a cikin Tsakiyar Birnin Accra da ke Ghana.
  • 1957 - 1961: Lancing College, Sussex, England.
  • 1964 – 1967: University of Ghana (B.Sc. Econ).
  • 1771/1775: Kira Zuwa Dandamalin Lauyoyi (Call to bar) a UK da Ghana.

Gogayyar Aiki

  • 1962 – 1964: Malamin Makaranta a Accra Academy Secondary School.
  • 1971 – 1975: Aikin Lauya a ofishi mai suna Coudert Brothers da ke Ƙasar Faransa.
  • 1975 – 1979: Aikin Lauya a ofishi mai suna U.V. Campbell, Accra, Ghana.
  • 1979: Founded Premphe & Co., Accra, Ghana.
  • 1997: Elected to the Ghanaian Parliament.
  • 2001 – 2003: Attorney-General and Minister of Justice.
  • 2003 – 2007: Minister of Foreign Affairs.

Fafutikar Ƙwatar ‘Yancin

“Kowa yana yi masa kallon mutum ɗaya tilo da zai iya kawo ƙarshen rashawa”, a bisa yadda African News (2020) suka ruwaito Kwesi Jonah, manazarci a Makarantar Koyon Shugabancin Siyasa da ke Ghana.

Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, jajirtaccen ɗan fafutikar kishin ƙasa ne abin da ake ganin ya yi gado daga mahaifinsa Edward Akufo-Addo wanda yake turke ne daga cikin Turaku Shidan Ghana.

Nana Akuffo-Addo, ya bayar da gagarumar gudunmawa ta fuskacin fafutikar fitar da Ƙasar Ghana daga halin-koma-baya. Daga cikin kalamnsa na baya-bayanan akwai cewa: “Dimokuraɗiyya da ‘yanci, suna samarwa siyasa, walwala da tattalin arziƙi tsanin cigaban da Afirka ta daɗe tana jira”, jawabin da ya gabatar a ranar 27 ga watan Satumba na shekarar 2018 a babban ɗakin taro na jami’ar Yale da ke Tarayyar Amurka kamar yadda muka naƙalto daga Guzman (2018).

Tun kafin wannan rana kuwa, gudunmawar da Shugaba Nana Akuf-Addo ya bayar ba za ta lissafu ba. Amma, muhimmai ababen tinƙaho sun haɗa da:

  • 1978 - 1979: Babban Sakataren Ƙungiyar fafutikar ‘yanci mai suna People’s Movement for Freedom and Justice (PMFJ), ƙungiyar da ta taka muhimmiyar rawa wajen kawar da gwamnatin soji tare kuma da dawo da ƙasar Ghana zuwa turbar dimokuraɗiyya a shekarar 1978 - 1979
  • 1991 – 1992: Ya shugabanci Kwamatin Tsare-Tsare ne Ƙungiyar Tunawa da Danquah-Busia, wato Danquah-Busia Memorial Club, wadda ke da manufa ta adana tarihi da gudunmawar waɗannan fitattun gwarazan dimokuraɗiyyar Ghana.
  • 1992: Ya kafa jarida mai zaman kanta wadda aka kira Statseman, wadda daga baya ta zama muryar sabuwar jama’iyyar NPP a fakaice.

Siyasa

Nana Akufo-Addo tun shekarun 1970s yake siyasa, (Deutsche Well International, 2021). A gidan siyasa aka haife shi don haka da ita ya tashi. Gidansu da ke Swalaba a Accra, babban birnin Ghana, shi ne cibiyar jama’iyyar siyasar fako a Ƙasar Ghana, wato jama’iyyar UGCC. Kuma uku daga cikin waɗanda suka kafa jama’iyyar, waɗanda kuma suke cikin Turaku Shida na Ghana ‘yanuwansa ne na jini kai tsaye; J.B Danquah ƙanin kakarsa ne, William Ofori, kawunsa ne sai kuma Edward Akufo-Addo wanda shi ya haife shi. Saboda haka ya riƙe muƙaman siyasa da suka haɗa da:

  • Babban Jami’in Tsare-Tsare na Ƙasa na Jama’iyyar NPP a Kakar Zaɓe ta shekarar 1992.
  • Shugaban Yaƙin Neman Zaɓen Ɗantakarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jama’iyyar NPP na shekarar 1992, Farfesa Albert Adu Boahen.
  • Jagoran Alliance for Change (AFC), 1995.

Takarar Shugabancin Ƙasa

  • 1998: Nana Akufo-Addo ya fara nuna sha’awarsa ta neman takarar shugabancin ƙasa a shekarar 1998, a Jama’iyyarsa ta NPP amma bai kai ga nasara ba inda abokin karawarsa, John Kufuor ya yi nasara a kansa.
  • 2007: Nana Akuof-Addo ya sake nuna sha’awarsa ta neman takara a karo na biyu a Jama’iyyarsa ta NPP, inda ya samu kashi 48 cikin ɗari na ƙuri’un da aka kaɗa a lokacin zaɓen fidda gwani daga cikin mutane 16. Daga baya aka yarje masa aka bashi takara.
  • A kakar babban zaɓen Ghana na shekarar 2008, ya samu gagarumar nasarar cin mafiya rinjayen dukkan ƙuri’un da aka kaɗa, inda ya samu ƙuri’u miliyan huɗu da dubu ɗari biyar da ashirin da ɗaya da talatin da biyu (4,521,032). Wannan ta bashi damar samun kashi arba’in da tara da ɗigo goma sha uku (49.13%) cikin ɗari, wanda bai kai abin da ake buƙata ba na kashi hamsin cikin ɗari (50%) da ragowar ƙasa da kashi ɗaya (0.87%).

  • Nana Addo Dankwa Akufo-Addo a Kakar Yaƙin Nema Zaɓe
    Hoto:Graphics.com.gh
  • 2012: Ya sake tsayawa takara.
  • 2016: A karo na uku, Nana Akufo-Addo ya sake tsayawa takara abin da ya bashi nasarar kai wa ga kujerar shugabancin Ƙasar Ghana wanda yake kai a halin yanzu (2021).
  • 2020: Nana Akufo-Addo, ya sake tsayawa takarar zaɓen neman wa’adin mulki na biyu a kakar zaɓe ta 2020, takarar da ta bashi nasarar lashe zaɓensa a karo na biyu.

Shugabancin Ƙasa

A karon farko a tarihin siyasar Ghana, Nana Akufo-Addo ne ya fara cin zaɓe a zagayen farko da kashi hamsin da uku da ɗigo tamanin da biya (53.85%) na dukkan ƙuri’un da aka kaɗa. Adadin da ya haura abin da ake so da kashi uku da ɗigo tamanin da biyar (3.85%).

Auratayya


Nana Addo Dankwa Akufo-Addo Tare da Iyalansa
Hoto: Ghana TV Live

Shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya auri matar da yau ta zama Uwar-Gidan Shugaban Ƙasa (First Lady) ta Ghana, mai suna Rebecca, wadda ita kuma ‘ya ce ga Kakakin Majalisa na Jamhuriyar Ghana ta Uku, marigayi Mr. Justice J.H Griffiths-Randolph.

Suna da ‘ya’ya biyar (5) da jikoki biyar.

Wannan shi ne ƙarshen labarin Shugaba, Basarake, Fitaccen Lauya, Gogaggen Ɗansiyasa, kuma Jajirtaccen Ɗan Rajin Ƙwatar ‘Yanci, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo.

Lambobin Yabo da Girmamawa

Mai Girma Shugaban Ƙasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akuf-Addo, ya karɓi lambobin yabo da girmamawa masu tarin yawa daga ƙasashe da ƙungogiyoyi daban-daban a faɗin duniya. Kaɗan daga ciki su ne:


Nana Addo Dankwa Akufo-Addo Yana Karɓar Kyauta
Hoto:The Presidency Ghana
  • 2021: Ya samu lambar yabo mai taken “Grand Commander of the Republic of Sierra Leone”; wadda kuma ita ce lambar yabo mafi girma a Ƙasar Salo. Mai girma shugaban Ƙasar Salo, Julius Mada Bio shi ya rataya masa wannan lamba.
  • 2016: Princeton University (2019) sun ruwaito cewa ya karɓi yautar Mother Theresa International Memorial Award for Social Justice.
  • Manazarta

    African News (2021). The Pan-African Ghanaian President Nana Akufo-Addo An ciro a 2021 daga shafin: https://www.africanews.com/2020/12/04/who-is-pan-african-ghanaian-president-nana-akufo-addo/

    Embassy of Ghana SEOUL (2018). The President of Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo. An ciro a shekarar 2021 daga shafin: https://ghanaembassy.or.kr/en/?page_id=54

    Deutsche Well International. (2021). Ghana Election: Nana Akufo-Addo and his second term. An ciro a shekarar 2021 daga shafin: https://www.dw.com/en/ghana-election-nana-akufo-addo-and-his-second-term/a-55882901

    Ghana Web (2021). Nana Addo Dankwa Akufo-Addo. An ciro a 2021 daga shafin: https://www.ghanaweb.com/person/Nana-Addo-Dankwa-Akufo-Addo-253

    Guzman K (2018). Ghanaian President Nana Akufo-Addo Discusses Democracy and Development in Africa. An ciro a 2021 daga shafin: https://som.yale.edu/event/2018/09/president-of-the-republic-of-ghana-democracy-and-development-in-africa

    McKenna A. (2021). Nana Addo Dankwa Akufo-Addo President of Ghana. An ciro a 2021 daga shafin: https://www.britannica.com

    Princeton University (2019). A Public Conversation with His Excellency Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, President of the Republic of Ghana. An ciro a 2021 daga shafin: https://piirs.princeton.edu/event/public-conversation-his-excellency-nana-addo-dankwa-akufo-addo-president-republic-ghana

    The Presidency (2018). The President Nana Addo Dankwa Akufo-Addo. An ciro a shekarar 2021 daga shafin: https://presidency.gov.gh/index.php/governance/the-president

    University of Ghana Alumni (2021). Nana Addo Dankwa Akufo-Addo. An ciro a 2021 daga shafin:https://ar.ug.edu.gh/nana-addo-dankwa-akufo-addo

    Wikipedia (2021). Nana Akufo-Addo. An ciro a 2021 daga shafin: https://ar.ug.edu.gh/nana-addo-dankwa-akufo-addohttps://en.wikipedia.org/wiki/Nana_Akufo-Addo


    Shafin Tarihi
    Shafin Ghana
    Ƙabilun Ghana
    Yankuna Ghana

    Shugabannin Ƙasa



    Tarihin Ghana

    Haƙƙoƙin 'Yanƙasa

    ‘Yanƙasanci

    Haƙƙoƙi da ‘Yanci

    ‘Yancin Rayuwa

    'Yancin Walwala


    Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


    Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



    Sauran Shafukanmu:

    Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub